Amirka na fuskantar matsin lamba kan kisan Khashoggi
November 18, 2018Talla
A baya dai Saudiyya ta yi amai ta lashe game da wannan batu kafin a farkon wannan mako a jiyo maigabatar da kara masarautar na kokarin wanke Yarima Mohammed bin Salman kan wannan batu.
Kisan Jamal Khashaoggi mai shekaru 58 a karamin ofishin Saudiya da ke birnin Santanbul na kasar Turkiyya na zaman kalubale ga cigaban kawance tsakanin Amirka da kasar ta Saudiyya.