Khashoggi: Jamus ta kira jakadan Saudiyya a Berlin
October 22, 2018Talla
Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ce ta gayyaci jakadan Saudiyya da ke kasar, don tattauna batun da ke daukar hankali a duniya, wato kisan da aka yi wa dan jaridan Jamal Khashoggi.
Mai magana da yawun ma'aikatar Maria Adebahr, ta ce ganawar ce za ta tabbatar da matsayin gwamnatin Jamus kan batun mai matukar takaici.
A jiya Lahadi ne kuwa shugabar gwamnati Angela Merkel, ta bayyana cewa Jamus ta dakatar da sayar wa da Saudiyya da makamai.
Shugaba Erdogan na urkiyya dai ya yi alkawarin bayyana abin da ya faru dalla-dalla ga duniya, a ranar Talata.