Kiki-kaka a zaman shari'ar Habre na Chadi
September 11, 2015Ranar 20 ga watan Yulin da ya gabata ne dai kotun da ke da cibiyarta a birnin Dakar na kasar Senegal ta bude zaman shari'ar tsohon Shugaban mulkin kama karyar kasar ta Chad Hissene Habre wanda ake zargi da take hakin Dan Adam a lokacin milkinsa da ya yi daga shekara ta 1982 zuwa ta 1990. Sai dai a wannan rana tun ba a je ko ina ba kotun ta dage zaman shari'ar a sakamakon wani yamutsi da Habre din da tarin magoya bayansa da suka halarci zaman shari'ar suka tayar a kotun suna masu kalubalantarta da cewa ba ta da hurumin yi masa shari'a.
Lauyoyin Habre sun yi korafi
Kwanaki 45 bayan haka ne kotun ta sake bude zamanta a birnin na Dakar. Sai dai lamarin ya kasance ko bana 'yar bara inda tsohon shugaban kasar Chadin ya ki ya bayyana a zaman kotun inda ta kai sai da aka yi amfani da karfin tuwo wajen iza keyarsa zuwa gaban alkali. Kuma daya daga cikin lauyoyinsa ya nuna rashin jin dadinsa da wannan mataki ya na mai cewa.
"Abin da suke nan suna yi a yau wani zaman shari'a ne na wasan kwaikwayo domin bai wa lamarin suffa ta shari'ar gaske kan wani hukunci da ba tun yau ba aka rigaya aka yanke shi na kama Hissen Habre da laifi"
Lauyoyin mutanan da aka zalinta sun damu da kyaluwar Habre
Hissene Habre dai ya ki ya ce uffan sannan ya ki amincewa da ya dauki lauyoyi ko kuma ya amince da wadanda kotun ta bashi domin kareshi. Matsayin da lauyoyin mutanan da ya zalunta suka bayyanashi da na wasa da hankalin jama'a.
" Wannan na nufin Hissene Habre ya ki ya bada hadin kai ga kotun wacce ma ya ke bayyanata da cewa ba alkallai ba ne ta kunsa a a wani komitin ne kawai na jami'an gwamnati.Ka ga irin wannan ji da kai na nuni da cewa Hissen Habre ba ya son a bashi kariya".
Yanzu haka dai wannan shari'a da ake yi wa tsohon shugaban kasar Chadi din ta haifar da mahawara dama rarrabuwar kawuna tsakanin 'yan Afrika masu ganin aiwatar da ita ya dace da kuma masu ganin akasin haka. Mamadu Lamine Ba wani dan jarida a kasar Senegal ya yi tsokaci dangane da yanda 'yan kasar Senegal ke kallon wannan shari'a
"Akwai 'yan kasar Senegal da ke ganin lallai Hissene Habre ya aikata duk laifukan da ake zarginsa da aikatawa dan haka ya kamata ya gurfana a gaban kuliya ya kuma yi kaso. Amma wasu na ganin wannan shari'a na zama hannunka mai sanda na kasashen yamma ga shugabannin kasashen Afrika masu niyar hana masu ruwa gudu a kokarinsu na morar arzikin Afrika kamar yanda shi Hissene Habre ya hana masu hakar man fetir na yankin Aouzou wanda ya yi dalilin yakin da ya abku tsakanin Chadi da Libiya a wancan lokaci
Yanzu haka wannan zaman shari'a ya ci gaba da gudana inda a halin yanzu shaidu ke bayyana daya bayan daya a gaban kotun suna sanar da ita abunda suka shaida Hissene Habre din ya aikata a lokacin milkin nasa.