Kim da Trump sun kama hanyar fahimtar juna
February 28, 2019Talla
Shugaba Kim dai na Koriya ta Arewa ya yi na'am da wannan bukata ta samar da ofishin tuntuba lokacin da yake bayani ana fassarawa yayin taron manema labarai a birnin Hanoi. Trump ya kara da cewa wannan mataki ne da zai kara matso da kasashen biyu su fara tafiyar da harkoki tare a hukumance. Kuma babbar nasara ce a cewar Trump.
Babban burin tattaunawar ta birnin Hanoi na Vietnam dai na zama dorawa a matakai na ganin an kai ga gabar da za a hana kasar ta Koriya ta Arewa mallakar makamai na nukiliya, ganin yadda kasar ke zakewa a gwaje-gwajen makamai da ke barazana ga tsaron duniya, sai dai Shugaba Kim ya ce da ba shi da aniya ta wargaza shirin makaman nukiliyar da ba ma zai halarci taron na Hanoi ba.