Kira ga kawo karshen rikicin kasar Libiya
December 17, 2014Talla
Fiye da shekaru uku bayan da kungiyar tsaro ta NATO ta kaddamar da matakin sojan da ya haddasa kifar da Gwamnatin marigayi Mouammar Kadhafi, har kawo yanzu wannan kasa na cikin tsaka mai yuwa sakamakon rashin samun wata tsayayyar gwamnati da zata hada kan 'yan kasar.
Wannan matsala ta baiwa dubban 'yan ta'adda damar kafa sansanoninsu a wannan kasa, inda a halin yanzu su ke ci gaba da kasancewa barazana ga kasashe kamar su Mali, Nijar da kuma Chadi. Da yake maga kan wannan batu, Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita cewa yayi muddin dai ba'a kawo karshen matsalar kasar ta Libiya ba, to baza'a samu kwanciyar hankali ba a yankin Sahel.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu