Kiraye-kirayen kawo karshen yaki a Sudan
July 11, 2023Talla
Kungiyar HRW da ta himmata wajen kare hakkin bil Adama ta ce a karshen watan mayu kadai, an kashe mutane da dama tare da jikkata dubbai a lokacin da mayakan RSF da kabilun Larabawa suka kai hari a Darfur. Dama dai rahotanni sun nunar da cewa hare-hare ta sama na sake girgiza Khartum babban birnin kasar Sudan.
Sai dai kungiyar Igad ta kasashen gabashin Afrika da Sudan take ciki, ta yi kira da a tsagaita bude wuta ba tare da wani sharadi ba, a taron wanzar da zaman lafiya da ke gudana a Addis Ababa. Amma masana tsaro na ganin cewar jagororin yakin Janar al-Burhane da Janar Hamdane Daglo sun zabi neman nasara ta hanyar yaki maimakon tattaunawa don samar da masalaha.