Kisan gila a kan fararan hula a Sudan ta Kudu
February 1, 2016Talla
Rahoton wanda wata hukuma ta ƙasa da ƙasa wacce ke kula da saka ido a kan mutunta yarjejeniyar da aka cimma tsakanin shugaba Salva Kiir da tsohon matamaikinsa Riek MaChar ta bayyana a yau.
Ta ce,ta miƙashi ga ƙungiyar Tarrayar Afirka a lokacin da ta gudanar da taronta a ƙarshen mako a Adis Ababa.a Kasar ta Sudan ta Kudu jami'an tsaro sotari sukan yin amfani da kontina domin kule fursunoni masu laifi ba tare da yin la'akari ba da irin tsananin gumi da ke a cikin kontinar ba.Har ya zuwa yanzu dai gwamatin ta Sudan ta Kudu ba ta ce ufan ba a kan wannan zargi.