Dakarun Iraki sun hallaka 'yan IS
October 11, 2015Talla
Mahukutan Irakin sun sanar da cewa sojojin samansu sun kai farmaki a kan mayakan IS din a yayin da suke taro a wani gari da ke yammacin Irakin, kana sun yi barin bama-bamai a kan ayarin motocin jagoran kungiyar Abu Bakr al-Baghdadi a yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa wajen taron, sai dai sun ce an dauke shi daga cikin ayarin ba tare da sun san yanayin da yake ciki ba. Wani mayakin IS din ya tabbatar da aafkuwar harin, ko da yake bai bayyana takamaiman halin da Baghdadi ke ciki ba sai dai ya ce koda an kashe shi ba yana nufin an kashe IS ba ne domin kuwa za su ci gaba da yakin da suke.