1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin kafa gwamnatin hadin kan kasa a Isra'ila

September 19, 2019

Tana kasa tana dabo a zaben 'yan majalisar dokokin Isra'ila bayan da aka gaza samun gwani a zaben tsakanin Firaminista Benjamin Netanyahu da kuma tsohon hafsan hafsoshin soji Benny Gantz.

https://p.dw.com/p/3PtWG
Benny Gantz da Avigdor Lieberman da kuma Benjamin Netanyahu
Benny Gantz da Avigdor Lieberman da kuma Benjamin NetanyahuHoto: Reuters/R. Zvulun

Yanzu haka tana kasa tana dabo a zaben 'yan majalisar dokokin kasar Isra'ila da aka gudanar a farkon wannan mako bayan da aka gaza samun gwani a zaben tsakanin Firaminista Benjamin Netanyahu da kuma tsohon hafsan hafsoshin sojin kasar Benny Gantz wanda babu wanda ya samu rinjaye a majalisar domin zama shugaban gwamnati. Mutum na uku wanda zai iya zama raba gardama a zaben idan har ba a kafa gwamnatin hadin kan kasa ba shi ne tsohon ministan tsaro Avigdor Lieberman.

Avigdor Lieberman wanda ake yi wa kallon dan siyasa mai tsaurin ra'ayi bai amince da gama addini da mulki ba.

An haifi Avigdor Lieberman a cikin watan Yuni na shekara ta 1958 a Kichnev a Moldaviya cikin tsohuwar Tarrayar Sobiet. Ya karanta fannin aikin gona da sauran fannonin da suka hada da huldar kasa da kasa. Kana ya yi aiki na wani dan lokaci a birnin Baku a kasar Azerbejan kafin a karshen shekara ta 1970 iyalansa su yi kaura tare da shi zuwa Isra'ila. Ya fito ne daga zuri'ar Yahudawan Rasha.

Wahlen in Israel - Avigdor Lieberman
Hoto: Getty Images/AFP/J. Marey

Ya rike mukamai da daman na ministoci dabam-dabam har ma da na mataimakin firaminista kana ya kasance daya daga cikin shika-shikan jam'iyyar Likud da ke kan mulki wato jam'iyyar Firaminista Benjamin Netanyahu, kafin a shekara ta 1999 ya kafa jam'iyyarsa ta Yahudawa masu asali daga kasar Rasha wacce ake kira da sunan Israel Beteynou. A cikin watan Nuwamba na shekara ta 2018 ya yi marabus daga matsayin ministan tsaro bayan da Isra'ila ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Hamas da yake dauka a matsayin 'yan ta'adda. Hakan ya sa jam'iyyarsa ta fice daga kawancen jam'iyyun siyasar da ke yin mulki wanda da ma a lokacin dangantaka tsakanin jam'iyyun siyasar biyu ta yi tsami.

A zaben da aka yi zagaye na farko na 'yan majalisar dokoki a cikin watan Afrilu da ya gabata jam'iyyarsa ta samu kashi 4 cikin 100. Kuma a lokacin da aka shiga tattaunawa don yin kawance tsakaninsu da jam'iyyar da ke kan mulki ta Likud an watse hannun riga bayan da Liebeman ya bukaci da dalibai Yahudawa yan Orthodox da a rika sakasu aikin soji na bautar kasa abin da jam'iyyar Likud ta ki amincewa da shi

Larissa Ramennick wata mai fashin baki ce a kan al'amuran siyasa tab yi tsokaci tana mai cewa.

"Shi kadai ne dan siyasa na Isra'ila da ke fafutukar ganin ya hana kafa gwamnati a karkashin tsarin dokoki na addinin Yahudu abin da yake so shi ne yin kawance ba tare da jam'iyyun siyasa masu alaka da addini ba."

Yanzu haka dai sakamakon yadda babu wanda ya samu rinjaye a zaben 'yan majalisar dokokin, ana gani idan har ba a samu kafa gwamnatin hadin kan kasa ba tsakanin Benjamin Netanyu da Benny Ganzt, to jam'iyyar Avigdor Lieberman, wacce ta zo ta uku a zaben za ta iya zama raba gardama ga duk wanda ta mara wa baya domin samun rinjaye.