1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kamarin cin-hanci da rashawa

Uwais Abubakar Idris
December 19, 2024

Hukumar Yaki da Cin-hanci da Rashawa da Aikata Manyan Laifuka ta Najeriya ICPC, ta sanar da bankado zargin sama da fadi na makudan kudi ta hanyara almundahana da ke durkusar da tattalin azikin kasar.

https://p.dw.com/p/4oNkN
Najeriya | Cin-hanci | ICPC | EFCC
An jima ana bayyana yadda ake asarar makudan kudi sakamakon cin-hanci a NajeriyaHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Bincike ne dai da Hukumar Yaki da Cin-hanci da Rashawa da Aikata Manyan Laifuka ta Najeriya ICPC ta yi, ta ce ya kaita ga bankado zargi na cin-hanci da rashawa masu ban mamaki daga bangarorin da ba a ma tsamanin wannan mumunar barna na faruwa. Daga ciki shi ne yadda aka karkatar da makudan kudi da aka kebe, domin biyan ma'aikatan boge a sassan gwamnati. A daya bangare na aikin da ta yi shi ne bibiyar ayyukan mazabu da a kan bai wa 'yan majalisar dokokin Najeriyar, wanda a wasu lokuta ake samun zargin ana karkatar da kudin. Hukumar ta ce, wannan ya sanya  ta samu nasarar toshe kafar zurarewar kudin da suka kai biliyan 30. Muni da illara da wannan matsala ta cin-hanci da rashawa ke yi ga tattalin arzikin Najeriyar, na da yawan gaske. Satar da masu halin bera suka yi wa kasar an kiyasta cewa ta kai dalar Amurka bilyan 550, kusan adadin kasafin kudin Najeriyar na shekaru bakwai a jere. Duk da nasarorin da ake samu, akwai kalubale na daukar lokaci ana shari'ar wadanda ake zargi da ke kawo cikas ga yakar cin-hancin a kasar. A baya dai an yi koken rashin hadin kai da ke haifara da karo da juna a tsakanin hukumomin yaki da cin-hancin, musamman na ICPC da EFCC. Daya daga cikin matsalolin da har yanzu yaki da cin-hanci da rashawa na Najeriyar ke fuskanta shi ne rashin dokar da ke samar da kariya ga masu tonon silili a kasar, abin da ya sanya masu tona wadanda ake zargi suka ragu sosai. To sai dai duka shugabanin hukumomin ICPC Daktar Musa Aliyu da EFCC Ola Olukayode sun bayyana cewa, akwai bukatar majalisa ta hanzarta amincewa da dokar da ke gabanta kan batun.