Jamus ta gargadi Isra'ila a kan kogin Jodan
June 10, 2020Talla
A ziyararsa ta farko da ya kai a wata kasar ketare tun bayan bullar cutar corona, Heiko Maas ya ja kunnen Isra'ila da kada ta kuskura ta aiwatar da kudurinta na mamaye yankin nan na yamma da kogin Jodan wanda a cewarsa hakan wani kokari ne na yi wa dokokin kasa da kasa karan tsaye.
Mr Maas din ya fito karara ya soki lamirin na Isra'ila wanda ya ce Jamus da kungiyar Tarayyar Turai ba su amince da abin da Isra'ilar ke kokarin aikatawa ba.
Yunkurin dai na Isra'lar na zuwa ne a daidai lokacin da Jamus ke shirye-shiryen karbar jagorancin kungiyar Tarayyar Turan na karba-karba da kuma kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya nan da 1 ga watan Yuli mai kamawa, wanda wannan ranar ce Isra'ila ta tsaida domin kwace yankin.