Kokarin karbe garin Tikrit daga hannun IS
March 5, 2015Talla
Shaidun gani da ido dai sun ce mutane da dama sun rasa rayukansu a wannan gumurzu da ake musamman ma lokacin da 'yan bindinga suka afkawa yankunan da fararen hula suka fi yawa.
Dubban mutane ne dai aka yi hasashen za su rasa matsugunansu sakamakon wannan rikici da ake yi. A watan Yunin bara ne dai garin na Tikrit ya fada hannun 'yan kungiyar nan ta IS da ke rajin kafa daular Islama a Irakin da Siriya.