1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin kawar da mayakan IS daga Libiya

Ahmed SalisuJune 10, 2016

Amirka ta jinjina wa dakarun gwamnatin Libiya bayan da suka kutsa kai cikin garin nan na Sirte a wani yunkuri na kawar da 'yan kungiyar IS da suka kame shi.

https://p.dw.com/p/1J456
Libyen Sirte Militär IS
Hoto: Getty Images/AFP/H. Turkia

Mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Amirka ta Pentagon Peter Cook ya ce Amirka ta ji dadin wannan namijin kokari da sojin na Libiya suka yi wanda ce hakan na nuna ci-gaban da aka samu musamman a bangaren gwamnatin hadin kan kasa da ke rike da madafun iko.

Gwamnatin Libiya ta bakin kakakin dakarun da ke wannan gumurzu da 'yan IS ta ce yanzu haka sojojinta na tsakiyar birnin na Sirte kuma suna sa ran karbe iko da shi nan da 'yan kwanakin da ke tafe. Birnin na Sirte dai wanda shi ne mahaifar tsohon shugaban kasar Mu'ammar Gaddafi ya kasance wata tunga ta 'yan IS tun bayan da suka shiga kasar da nufin mayar da wani bangare nata karkashin daularsu.