1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin shawo kan rikicn Sudan ta Kudu

Umaru AliyuDecember 26, 2013

Shugaban kasar Kenyan Uhuru Kenyatta da kuma Firaministan Habasha Hailemariam Desalegn, sun isa kasar Sudan ta Kudu domin tattaunawa da bangarori biyu dake gaba da juna a kasar, da nufin kawo sulhu a tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/1Ah7D
Hoto: picture-alliance/dpa

Sama da mako guda ke nan da aka fara bata kashi a kasar Sudan ta Kudu tsakanin kabilu magoya bayan shugaban kasar Salva Kiir, da kuma masu goyon bayan tsohon mataimakinsa da ke zaman babban abokin adawarsa Riek Machar ba tare da samun wata maslaha ba.

Wani kiyasi na Majalisar Dinkin Duniya ya nunar da cewa a kalla mutane sama da dubu 80 ke neman mafaka a sansanin dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dake Juba fadar gwamnatin Sudan ta Kudu, yayin da wasu sama da dubu 20 suka warwatsu a sassa daban-daban na kasar. Tuni dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka fara bayyana damuwarsu kan wannan rikici, da yake neman juyewa izuwa yakin basasa a kasar dake zama 'yar jaririya a duniya baki daya, kamar yadda Marina Peter mamba a wata kungiyar kare hakkin dan Adam mai suna Sudan Focal Point ta shaidawa tashar DW cewa idan aka yi sake rikicin zai ci gaba da ta'azzara.

"Wannan rikicin dake tsakanin tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar da kuma Shugaba Salva Kiir ba wai rana guda ya taso ba, abu ne da ya dade yana naso har ya girmama, tsahon shekara guda kenan da dangantaka ta ke ci gaba da yin tsami a tsakaninsu. Babban tashin hankalin a nan shine, da farko rikicine kawai tsakanin wasu tsofaffin mutane guda biyu da ko wannensu ke son ci gaba da zama kan madafun iko, amma a zahirin gaskiya yanzu rikicin ya kazanta".

Südsudan Juba Riek Machar Salva Kiir 09.07.2013
Shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek MacharHoto: Reuters

Dakarun wanzar da zaman lafiya ka iya samun cikas

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban-Ki moon ya bukaci da a kara yawan dakarun wanzar da zaman lafiya dake Sudan ta Kudun domin shawo kan kara lalacewar al'amuran da ake samu a kasar. Sai dai a cewar Marina Peter, ta ce yana da kyau hakan, amma sai sunyi taka tsan-tsan domin gujewa yin baya ba zani.

"Yana da kyau su kasance da yawa, kuma ya zama wajibi su rinka gudanar da sunturi a sassa daban-daban na kasar, domin su nuna musu cewa suna nan kuma ba za su barsu su ci gaba da kashe mutane ba gaira ba dalili ba. Sai dai kuma wani lokaci zai zo da za su zamo ba za su iya tabuka komai ba, musamman ma idan al'amura suka ci gaba da tabarbarewa"

Kasar Sudan ta Kudu dai ta samu 'yancin kanta daga Sudan a shekara ta 2011 bayan da suka kwashe tsahon shekaru suna gwabza fada. A wani jawabi da ya yi Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudun ya ce baya bukatar tarihi ya sake maimaita kansa a kasar.

Südsudan Juba Flüchtlinge Tomping United Nations base
'Yan gudun hijira a sansanin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin DuniyaHoto: Reuters

Fargabar sake tsunduma cikin yakin basasa

"Ina so na tabbatar muku da cewa zaman lafiya ba yaki ba, fata na gari ba mugu ba za su tabbata a kasar nan. Al'ummarmu sun sha matukar wahala na tsahon lokaci da muka kwashe muna nemarwa kanmu 'yanci. A dangane da haka bana son na sake ganinsu sun kara komawa gidan jiya".

Majalisar Dinkin Duniya dai na ci gaba da nuna damuwa kan yadda al'amura ke kara kazanta a Sudan ta Kudun, inda sakatare janar na Majalisar Ban-Ki moon ya bukaci bangarorin biyu dake gaba da juna da su sasanta tsakaninsu domin kasar ta samu zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ita ma dai kungiyar hadin kian Turai wato EU ta nuna damuwarta a dangane da halin da ake ciki a Sudan ta Kudun musamman ma yadda kungiyar ta ce ana ci gaba da kashe mutanen da ba su ji ba su gani ba.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani

Nuna karin labarai