Kungiyar kasashen gabashin Afirka IGAD ta kara wa'adin da ta debarwa bangarori biyu da ke yakar juna a Sudan ta Kudu na Shugaba Salva Kiir da kuma tsohon mataimakinsa Riek Machar, na su kawo karshen rikicin da ke tsakaninsu tare da kafa gwamnatin hadin kan kasa.