Koma-baya kan warare rikicin Isra'ila da Falasdinu
May 17, 2021Talla
Kudurin da China da Tunisia da Norway suka gabatar a zaman kwamitin sulhu na Majalisar ta Dinkin Duniya kan rikicin ya gamu da cikas ne bayan da Amirka ta ki amincewa da shi wanda shi ne karo na uku da ta yi hakan tun bayan da aka fara rikcin.
Kudurin dai ya bukaci da a kawo karshen tada kayar baya da mutunta dokoki na kasa da kasa na kare hakkin dan Adam da kuma daukar matakai na kare fararen hua musamman ma yara kanana.
Amirkan a share guda ta ce tana aiki ne ta karkashin kasa wajen ganin an warware rikicin cikin ruwan sanyi sai dai kin amincewar da ta yi da kudurin na yau ya sanya wasu daga cikin kawayen cika da mamaki duba da yadda lamura ke ci gaba da chabewa.