1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Komawa tattaunawa tsakanin Isra'ila da Hamas

August 12, 2014

A wani mataki na neman kawo karshen rikicin dake wakana a gabas ta tsakiya, tsakanin Isra'ila da Hamas, an koma Tattaunawa a kwanaki na biyu na tsagaita wuta.

https://p.dw.com/p/1Ct6f
Hoto: Khaled Desouki/AFP/Getty Images

Tawagogin Isra'ila da na Falesdinu sun koma fagen tattaunawa a wannan Talatar (12.08.2014) a birnin Alkahira na kasar Masa yayin da aka shiga kwanaki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma dan tattaunawar. sai dai tattaunawar da ba ta keke da keke ba dake kalkashin kulawar hukumomin kasar ta Masar, na da wahalar gaske da kuma gajiyarwa a cewar masu shiga tsakanin.

Wakillan bengarorin biyu, tare da masu shiga tsakani kan rikicin na Isra'ila da Hamas, na kokarin samun cimma yarjejeniyar mai dorewa dan ganin an kawo karshen wannan fada da a halin yanzu yayi sanadiyar rasuwar Falesdinawa kusan 2000, sakamakon lugudan wutar da Isra'ila tayi musu tun daga ranar 8 ga watan Yuli da ya gabata.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu