1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Bukatar hukunta masu laifuka

Gazali Abdou Tasawa
December 18, 2019

Wasu kungiyoyin kare hakin dan Adam sun yi kira ga gwamnatin rikon kwarya ta kasar da gaggauta gurfanar da mutanen da ke da hannu a kisan jam'a a yankin Darfur a gaban kuliya shekaru 16 bayan barkewar yakin kasar.

https://p.dw.com/p/3V0x7
Sudan Khartum | Prozess & Urteil Omar al-Baschir, ehemaliger Präsident
Hoto: picture-alliance/Anadolu Agency/M. Hajaj

 A cikin wani rahoto da suka fitar kungiyoyin da suka hada da Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Duniya sun zargi gwamnatin rikon kwaryar kasar ta Sudan da kin nuna azama wajen gurfanar da masu laifin a gaban kuliya.

 Kungiyoyin sun nuna rashin jin dadinsu dangane da yadda suka ce shekaru 10 bayan da kotun hukuntan manyan laifuka ta duniya ta bayar da sammacin kamo Shugaba Omar el-Bashir da wasu mukarrabansa guda uku a bisa zargin aikata laifukan yaki da na ci zarafin dan Adam da kuma aikata kisan kiyashi a Darfur, har yanzu aka kasa gurfanar da su a gaban kotun.

 Gwamnatin rikon kwaryar kasar ta Sudan wacce aka kafa bayan faduwar gwamnatin Shugaba Omar el-Bachir ta yi tun a wancen lokaci alkawarin maido da zaman lafiya a yankunan da ke fama da rikici a kasar musamman yankin Dafur inda wani kazamin yaki da ya hada 'yan tawaye da sojojin gwamnati ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 300, da raba wasu mutanen miliyan biyu da rabi suka tsere daga gidajensu in ji Majalisar Dinkin Duniya.