1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Batun juyin mulki da ma'aikata a Turkiya

Lateefa Mustapha Ja'afarJuly 18, 2016

A Turkiya an kori sojoji kusan 9,000 daga mukamansu, an kuma an kori ma'aikatan gwamnati 8,777 ciki har da gwamnoni 30 da jami'an 'yan sanda 52 daga aiki, bisa zargin su da hannu a yunkurin juyin mulki.

https://p.dw.com/p/1JR6L
Babban wanda ake zargi da kitsa juyin mulki a Turkiya Akin Öztürk
Babban wanda ake zargi da kitsa juyin mulki a Turkiya Akin ÖztürkHoto: picture-alliance/dpa

Kamfanin dillancin labaran kasar Anadolu ya ruwaito cewa tun bayan yunkurin juyin mulkin da sojojin kasar suka yi da bai yi nasarar ba kawo yanzu, an cafke akallah mutane 1000 ciki kuwa har da manyan hafsoshin sojan kasa da na ruwa. Firaministan kasar ta Turkiya Binali Yildirim ya bayyana cewa kawo yanzu sun cafke mutane 7,543 da suke zargi da hannu a yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba da suka hadar da dakarun sojojin kasar 6,038 da kuma lauyoyi da masu rajin kare hakkin dan Adam 755 da kuma daruruwan jami'an 'yan sanda. A cewar Yildirim mutane 208 sun yi shahada, yayin da kuma aka kashe wasu 'yan tawayen da suka yi yunkurin kifar da gwamnati Shugaba Raceep Tayyip Erdogan na Turkiyan 308. A wani labarin kuma kamfanin dillancin labaran kasar Analodu ya ruwaito cewa babban wanda Turkiyan ke zargi da kitsa juyin mulkin, wanda ya kasance tsohon hafsan sojojin sama na kasar Akin Öztürk ya amsa cewa yana da hannu dumu-dumu a yunkurin juyin mulkin, kuma ya yi hakan ne domin kwace iko. Öztürk dai ya amsa laifin nasa ne a yayin da yake amsa tambayoyin babban mai shigar da kara na kasar ta Turkiya.