1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Koriya ta Arewa ta yi gwajin sabon makami mai linzami

Mouhamadou Awal Balarabe
January 7, 2025

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un, wanda ya halarci harba makamin tare da 'yarsa Ju Ae ya ce wannan sabon makami mai cin matsakaicin zango "zai hana dukkan abokan gaba iya shafar tsaron kasarsa."

https://p.dw.com/p/4otHu
Koriya ta Arewa tana yawan gwajin makamai masu linzami
Koriya ta Arewa tana yawan gwajin makamai masu linzamiHoto: Yonhap/picture alliance

Koriya ta Arewa ta bayyana cewa ta yi nasarar gwada wani sabon makami mai linzami mai cin matsakaicin zango, don dakile take-taken abokan gaba a yankin Pacific.  An yi wannan gwajin ne a ranar litinin a daidai lokacin da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken yake tsaka da ziyara a Koriya ta Kudu da Japan, kuma makonni biyu kafin rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban Amurka.

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un, wanda ya halarci harba makamin tare da 'yarsa Ju Ae ya ce  wannan sabon makamin "zai hana dukkan abokan gaba iya shafar tsaron kasarsa." Wannan dai shi ne karon farko da Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami a shekarar 2025, wanda ya yi tafiyar kilomita 1,500 daga yankin Pyomgyang,  kafin ya fada cikin teku. Manazarta na ganin kaddamar da wannan makami mai linzami a matsayin sako ga shugaban Amurka na gaba.