Rasha; An daure jagoran adawa
August 27, 2018Talla
Alkali Alexei Stekliyev na kotun lardin Tverskoy a Rasha ya yanke hukuncin ne na zaman kaso tsawon kwanaki 30 ga Navalny saboda yadda yake yawan kiran gangamin adawa da gwamnati a bisa tsarin da ya saba wa dokar kasar ta Rasha inda a watan Janairu ya yi shelar gangamin adawa da mahukuntan na Rasha bayan kuwa ya san saba doka ne kiran gangami ba tare da sanar da ofishin magajin gari ba.
Kafin dai daukar wannan mataki na kotun dan adawar ya ce gabatar da shi a gaban kotun ma karan tsaye ne ga dimukuradiyyar Rasha.