Kotu ta ce a bude gidajen talabijin a Kenya
February 1, 2018Talla
'Yan jarida da 'yan fafutika sun koka da yadda gwamnatin ta rufe kafafan yada labaran daga ranar Talata. Wasu 'yan jaridar sun bayyana cewa sun boye kansu da kwana a ofisoshinsu don gudun kada su fito a kamasu.
Shi dai madugun adawa Raila Odinga ya rantsar da kansa a matsayin shugaban al'umma a kokarin nuna adawa da rantsuwar kama shugabancin Uhuru Kenyatta da aka bayyana da samun nasara a zaben da aka yi a shekarar bara.
Odinga dai ya ce zaben cike yake da kura-kurai a kasar ta Kenya da ke gabashin Afirka.