1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta dage ranar sake zaben Laberiya

Abdul-raheem Hassan
November 6, 2017

Kotun Kolin kasar Laberiya ta dage zaben shugaban kasa da za a sake gudanarwa a ranar bakwai ga watan Nuwamba, wannan mataki na zuwa ne bayan zargin magudi da dan takarar jam'iyar Liberty ya gabatar tun zagayen farko.

https://p.dw.com/p/2n8Ow
Liberia Monrovia Wahlen
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Babban alkalin da ya yanke hukuncin Francis Korkpor ya umarci hukumar zaben kasar da ta kaddamar da bincike kan tuhumar magudin zabe da dan takarar jam'iyar Liberty Charles Brumskine ya gabatar. Wannan hukuncin ya zo kwanaki biyar bayan da Kotun ta dakatar da dukkanin shirin gudanar da sake zaben ranar bakwai ga watan Nuwamba.

Dama dai za a shiga zagaye na biyu na zaben ne tsakanin tsohon dan wasan kwallon kafan kasar George Weah da ke jagorantar babbar jam'iyar hadaka ta CDC, da kuma mataimakin shugaban kasa mai ci a yanzu Joseph Boakai na jami'yar Unity Party.

A yanzu dai Kotun ba ta bada haske kan ranar da za sake gudanar da zaben shugaban kasar ba, amma dai ta ce tana jiran sakamakon bincike da zai fito daga hukumar zaben kasar.