1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta daure dan tsohon shugaban Angola

Mouhamadou Awal Balarabe
August 14, 2020

An yanke wa Jose Filomeno dos Santos wato dan tsohon shugaban kasa Jose dos Santos na Angola hukuncin daurin shekaru 5 a gidan yari bayan da ta same shi da laifin zamba da sama da fadi da dukiyar kasa.

https://p.dw.com/p/3gyd1
Angola Ex-Präsident Jose Eduardo dos Santos
Hoto: Getty Images/AFP/A. Rogerio

Kotun kolin Angola ta yanke wa Jose Filomeno dos Santos, dan tsohon shugaban kasa Jose Eduardo dos Santos hukuncin shekaru biyar a gidan yari, bayan da ta same shi da laifin "zamba cikin aminci" a lokacin da ya shugabanci Asusun ba da tallafi a tsakanin shekara ta 2013 zuwa 2018. Sannan kotun da ke da mazauninta a birnin Luanda ta yanke wa mukarranbansa uku hukuncin shekaru uku zuwa hudu a kurkuku bayan da ta same su da laifin karkatar da makudan kudade na babban bankin kasar. Sai dai an wanke mutum na hudu da ake tuhuma wanda da ma ya dade ya cewa ba shi da hannu a karkatar da dukiyar kasa.

Tun dai bayan sauka daga mulki da dos santos a 2017, shugaba Joao Lourenco ya sa kafar wando guda da duk wadanda suke da hannu a cin hanci da karbar rashawa, lamarin da ya sa aka tsige 'yar shugaba Jose dos Santos wato Isabel dos Santos daga mukaminta na shugabar kanfanin man fetur na kasar.