Kotun Senegal ta daure 'yan majalisar kasar
January 2, 2023Talla
Wata kotu a Senegal ta yanke wa wasu 'yan majalisar kasar maza hukuncin daurin watanni shida, saboda cin mutuncin wata 'yar uwarsu 'yar majalisa da ke dauke da juna biyu a farkon watan Disamba.
Lamarin ya faru ne lokacin da ake zaman majalisa inda aka samu musayar ra'ayi, abin da ya kai ga doke-doke a majalisar.
Mutanen da aka yanke wa hukuncin na dauri, da suka hada da Amadou Niang da Massata Samb dukkanin su daga jam'iyyar adawa ta PUR, za kuma su biya tarar CFA milyain biyar kwatankwacin dalar Amirka dubu takwas da 200 a matsayin diyya ga 'yar majalisar.
Wasu hotunan bidiyo dai sun nuno yadda 'yan majalisar ke dukan takwarar tasu Ndiaye Gniby, wadda ke cikin hadakar jam'iyya mai mulki a Senegal din.