Koto ta hana umarnin gwamnati a Kenya
December 14, 2021Talla
Gwamnatin Kenya ta bukaci jama'a su nuna shaidar allurar riga kafi, daga ranar 21 ga watan Disamba shekarar 2021 domin samun damar gudanar da ayyukan gwamnati da suka hada da asibitoci da makarantu da ofisoshin gwamnati. Sai dai alkalin babbar kotun kasar Antony Mrima ya dakatar da wannan umarni har sai an fara sauraron karar da wani dan kasuwa ya shigar, inda ya kira umarnin da "zalunci” da saba wa kundin tsarin mulkin kasar.
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch (HRW) ta soki umarnin a matsayin nuna wariya tare neman gwamnati ta yi watsi da shirin. Mutane miliyan 3 da dubu 200 suka kammala rigakafin cutar corona a Kenya, adadin ya gaza tsammanin gwamnati na yi wa mutane miliyan 27 kamin karshen shekarar 2022.