1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana tuhumar tsohon hafsan Najeriya da cin hanci

Kmaluddeen SaniMarch 7, 2016

Wata kotu a Tarayyar Najeriya ta ba da umurnin iza keyar tsohon babban hafsan tsaron kasar Air Marshal Alex Badeh zuwa gidan kaso.

https://p.dw.com/p/1I8bE
Tsoffin manyan jami'an sojan Najeriya, Alex Badeh a sahun gaba cikin shudin kaya.
Tsoffin manyan jami'an sojan Najeriya, Alex Badeh a sahun gaba cikin shudin kaya.Hoto: picture-alliance/AP

Shi dai Alex Badeh an tsare shi ne a watan Fabarairun da ya gabata bisa badakalar karkatar da sama da naira biliyan uku a shekara ta 2013 da ke zama kudaden da gwamnati ta tanada don tunkarar ayyukan magance matsalolin 'Yan Boko Haram.

Daga cikin tuhumomi 10 da ake masa dai sun hada da cin amana da kuma cire sama da naira biliyan daya daga cikin asusun rundunar sojoji domin amfanin kansa.

Tuni dai hukumar EFCC ta kwace wasu manya-manyan kadarorinsa da suka hada da gidaje a Abuja babban birnin Najeriya.

Tun dai lokacin da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya hau gadon mulki a shekarar data gabata yaci alwashin dukkanin wadanda suka yi watanda da kudaden gwamnati musamman ma kudaden da aka kebe don yakar kungiyar Boko Haram an gurfanar da su a kotu.