Kotu ta mayar da Zuma gidan fursuna
December 15, 2021Talla
A wannan Laraba wata kotu da ke kasar Afirka ta Kudu ta ba da umurnin ga tsohon shugaban kasar Jacob Zuma ya koma gidan fursuna, inda ta soke fitar da shi da aka yi saboda dalilan rashin lafiya a watan Satumba.
Zuma mai shekaru 79 da haihuwa an daure na watanni 15 saboda raina kotu na rashin bayyana a gabanta lokacin da aka tuhume shi da zargin cin hanci da rashawa.
Tuni tsohon shugaban na Afirka ta Kudu Jocob Zuma ya daukaka kara kan wannan umurnin kotu na ya sake komawa gidan fursuna a cewa tagowar lauyoyin da ke kare shi.