Kotu ta umurci ASUU da ta koma bakin aiki
September 21, 2022Talla
Mai shari'a Polycarp Hamman ya bukaci malaman jami'o'in su koma bakin aiki zuwa nan da dan lokacin da zai yanke hukunci a kan shari'ar da mahukuntan Najeriyar suka shigar da kara a gaban shi.
Sama da watanni 7 ke nan da aka rufe jami'o'i a Najeriya bisa neman karin albashi da kuma wasu alawus-alawus da malaman suka nema daga gwamnatin tarayya.
Wannan matakin na kotu dai na zuwa ne bayan da a jiya dali'bai a wasu sasan kasar suka gudanar da zanga-zangar neman a bude makarantu domin ci gaba da daukar darussa.