1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun Brazil ta ƙi miƙa Battisti ga Italiya

June 9, 2011

Hukumomin Shari'a na ƙasar Brazil sun sa ƙafa sun yi fatali da bukatar tasa ƙeyar Cesare Battisti zuwa Italiya bisa zargin kashe kashen bayin Allah a shekarar 1970.

https://p.dw.com/p/11XNG
Lokacin da jami'an tsaron Brazil ke kai Cesare Battistina kotu.Hoto: picture alliance/dpa

Kotun ƙolin ƙasar Brazil ta yi watsi da bukatar Italiya ta miƙa mata Cesare Battisti, wani tsohon ɗan yaƙin sunƙuru da ake zargi da aikata ta'asa a shekarun 1970. Tuni dai wannan hukunci ya haifar da tsamin dangantaka tsakanin ita Brazil da kuma Italiya da ta bayyana aniyar ɗaukaka ƙara a kotun ƙasa da ƙasa.

Shi dai Battisti da aka cafke a birnin Rio de Janairo a shekara ta 2007, ya arce ne daga gidan yarin Italiya a shekarar 1981 bayan an yanke masa hukunci ɗaurin rai da rai. Kotun ƙasar ta Italiya ta same shi da laifin kashe kashe bayin Allah a lokacin da ake damawa da shi a cikin ƙungiyar 'yan yaƙin sunƙuru, wacce ta ce ta na gudanar da ayyukanta domin ƙwanco wa 'yan rabbana ka wadata mu na Italiya hakkinsu, tare da yaɗa aƙidar komunisanci a ƙasar.

Battista ya ƙarya laifukan kisan kai da ake zarginsa da aikatawa, tare da danganta shi da wani bita da ƙulli na siyasa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Mohammad Nasiru Awal