1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun ICC ta sallami Laurent Gbagbo

Gazali Abdou Tasawa
January 15, 2019

Kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta kasa da kasa ta ICC ta wanke tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo da na hannun damarsa Charles Ble Goude, tare ma da ba da umurnin sallamarsu nan take. 

https://p.dw.com/p/3Bafz
Kombibild - Charles Blé Goudé und Laurent Gbagbo

Babban alkalin kotun ta ICC Cuno Tarfusser ya bayyana wannan hukunci a lokacin zaman da kotun ta yi kan bukatar da lauyoyin Gbagbo da Ble Goude suka shiga a gabanta ta neman sakin mutanen biyu.

Babban alkalin kotun ya ce da gagarimin rinjaye alkalan kotun suka amince da sakin mutanen biyu bayan da a cewar kotun, babban mai shigar da kara ya kasa gabatar da wadatattun hujjoji da doka ke bukata kan zarge-zagen da suke yi wa mutanen biyu. A dan haka ne kotun ta karbi bukatar neman sakin Gbagbon da Ble Goude tare da neman sakinsu nan take"

A gurfanar da Shugaba Gbagbo mai shekaru 73 a gaban kotun ta ICC a bisa zargin kasancewa ummulhaba'isan kisan jama'ar da ya wakana a rikicin da ya barke a kasar bayan da Gbagbon ya ki sauka daga mulki bayan da ya sha kayi a zaben 2010 zuwa 2011, rikicin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dubu uku a cikin watanni biyar kacal. 

Sai dai kotun ta ICC ta dakatar da sallamar mutanen biyu har ya zuwa gobe Laraba domin bai wa bangaren masu shigar da kara damar bayyana matsayinsu kan hukuncin. 

Laurent Gbagbo dai ya kasance wani tsohon shugaban kasa na farko da aka taba gurfanar da shi a gaban kotun ta ICC da ke da cibiyarta a birnin The Hague.