1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Izinin korar daraktan HRW a Isra'ila

Gazali Abdou Tasawa
November 6, 2019

Kotun kolin Isra'ila ta ba da izinin korar daraktan kungiyar kare hakkin dan Adam ta aksa da kasa ta Human Rights Watch daga cikin kasar a bisa zargin farfagandar kyamar Isra'ila

https://p.dw.com/p/3SVz3
Human Rights Watch Direktor Omar Shakir
Hoto: Getty Images/AFP/A. Momani

Kotun kolin Isra'ila ta ba da izinin korar daraktan kungiyar kare hakkin dan Adam ta aksa da kasa ta Human Rights Watch daga cikin kasar. Mahukuntan kasar ta Isra'ila dai na zargin Omar Shakir Ba'amarike da ke zama babban darakatan kungiyar ta HRW a Isra'ila da yankuanan Palasdinawa da kawo goyon bayansa ga farfagandar raba gari da Isra'ila.


A yanzu dai ya rage ga gwamnatin ta Isra'ila wacce dama tun a karshen shekara ta 2018, ta dakatar da takardar iznin zamansa a cikin kasar, da ta dauki matakin kora ko kuma kyale Mista Shakir a cikin kasar.


A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter jim kadan bayan bayyana hukuncin kotun, Daraktan kungiyar ta HRW a Isra'ila ya ce idan har gwamnatin isra'ila ta amince da aiwatar da matakin kotun, to kuwa ya rage masa kwanaki 20 daga yanzu ya fice daga cikin kasar wacce ita kuma za ta shiga sahun kasashe irin su Iran da Koriya ta Arewa da Masar wadanda suka dauki matakin haramta wa wakillan kungiyar ta HRW shiga cikinsu.