1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun kasar Angola ta daure 'yan adawa 17

Mouhamadou Awal BalarabeMarch 28, 2016

Bisa laifin yunkurin tawaye da yunkurin juyin mulki ne wata Kotu da ke birnin Luanda ta dogara wajen yanke wa wasu 'yan adawan Angola hukuncin dauri a gidan yari.

https://p.dw.com/p/1IL0Y
Provinzgericht in Luanda (Tribunal Provincial de Luanda)
Hoto: DW/N. Sul d'Angola

Wata kotu a kasar Angola ta yanke wa wasu 'yan adawa 17 hukuncin shekaru biyu zuwa takwas a gidan yari bayan da ta samesu da laifin tawaye da yunkurin juyin mulki. Tuni dai lawyan daya daga cikinsu ya bayyana cewar zai daukaka kara saboda a cewarsa bita da kullin siyasa ce.

Daukacinsu na neman shugaban kasa Jose Eduardo dos Santos da kada ya sake tsayawa takara bayan da ya shafe shekaru 36 a kan karagar mulki.Wasu daga cikin daurarrun sun shafe watanni suna yajin cin abinci a gidan yari, lamarin da ya hanasu halartar zaman kotun a wannan Litinin a birnin Luanda.

'Yan adawan Angola 17 na ci gaba da nesanta kansu daga zargin juyin mulkin da ake yi musu duk da cewa shugaba dos Santos ya rigaya ya bayyana cewar zai wanke hannunsa da harkokin siyasa a shekara ta 2018. dos Santos na Angola na daga cikin shugabbanin Afirka da suka yi kaurin suna wajen tursasa wa 'yan adawa a shekarun baya-bayannan.