1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

ICJ za ta yanke hukunci kan karar Afirka ta Kudu da Isra'ila

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
May 24, 2024

Afirka ta Kudu ta bukaci kotun ta hanzarta dakatar da Isra'ila daga kutsawa yankin kudancin Rafah sannan ta bada damar shigar da kayan agaji ga Falasdinawan da ke Gaza

https://p.dw.com/p/4gDnY
Hoto: Peter Dejong/AP Photo/picture alliance

A Juma'ar nan ce kotun Majalisar Dinkin Duniya ta ICJ za ta yanke hukunci kan rokon da Afirka ta Kudu ta yi mata na bada umarnin dakatar da yakin da Isra'ila ke yi a Gaza, bayan da ta zarge ta da kisan kare-dangi.

Karin bayani:ICJ ta yi watsi da bukatar karin kariya ga Falasdinawa

Afirka ta Kudu ta bukaci kotun ta hanzarta dakatar da Isra'ila daga kutsawa yankin kudancin Rafah sannan ta bada damar shigar da kayan agaji ga Falasdinawan da ke Gaza.

Karin bayani:Kotun MDD zata fara shari'ar Pretoria da Isra'ila kan Gaza

Isra'ila na fatan kotun za ta yi watsi da wannan bukata ta Afirka ta Kudu, tana mai cewar matukar ta tsagaita wuta daga yakin to kungiyar Hamas za ta samu damar sake farfadowa, har ma ta hana ta kubutar da Isra'ilawan da Hamas din ta yi garkuwa da su tun bayan harin ranar 7 ga watan Oktoban bara da ta kai wa Isra'ila.