1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kotun mulkin Mozambique ta tabbatarwa Frelimo nasarar zabe

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 24, 2024

Tarzomar da ta barke a cikin watan Oktoba ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 130 bayan arangama da 'yan sanda.

https://p.dw.com/p/4oXam
Masu zanga-zanga a birnin Maputo na Mozambique
Hoto: Amilton Neves/AFP

Kotun tsarin mulkin kasar Mozambik ta tabbatar wa jam'iyya mai mukin kasar Frelimo nasarar da ta samu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a cikin watan Oktoban da ya gabata, wanda ya janyo mummunar zanga-zanga a lokacin.

Karin bayani:Jagoran adawa na Mozambik ya shirya zaman kan teburin tattauna da shugaban kasar

Kotun tsarin mulkin kasar ce mai ikon karshe kan sakamakon, wanda ake kyautata zaton hukuncinta ka iya sake haddasa wata zanga-zanga a cikin kasar mai mutane miliyan 35, wadda Frelimo ke mulka tun a shekarar 1975 bayan samun 'yancin cin gashin kai.

Karin bayani:Zanga-zangar watsi da sakamakon zaben Mozambique

Tarzomar da ta barke a cikin watan Oktoba ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 130 bayan arangama da 'yan sanda.

Amurka na daga cikin kasashen da suka nuna fargabar mai ka je ya zo bayan wannan sanarwa ta kotun tsrin mulkin Mozambik, bayan da ta yi zargin cewa zaben da aka gudanar na cike da badakala iri-iri.