Kotun Senegal ta jaddada takarar Wade
January 30, 2012Kotun tsarin mulki a ƙasar Senegal ta kara tabbatar da shugaban kasa Abdoulaye Wade a matsayin ɗan takara a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 26 ga wata mai makamawa.
Tun daren Juma´ar da ta gabata ne, kotun ta bayyana jerin sunayen 'yan takara, amma jam'iyun adawa suka daukaka ƙara, domin ƙalubalantar takara Abdoulayei Wade.
Sannan kotun ta jaddada watsi da takara shaharraren mawaƙin nan Youssou Ndour da ta ƙarin wasu 'yan siyasa biyu.
Jam'iyun adawa sun yi kira ga magoya bayansu, su hito dafifi domin shirya zanga-zangar nuna adawa da takarar shugaba Abdoulaye Wade, da suka ce ta saɓawa dokokin tsarin mulkin ƙasar Senegal. A zanga zangar da suka shirya cikin daren juma´a dai, mutum guda ya rasa ransa.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita:Mouhamadou Awal Balarabe