1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kotun tsarin mulkin Afrika ta Kudu ta soke takarar Zuma

May 20, 2024

kotun kundin tsarin mulkin Afrika ta Kudu ta soke takarar Jacob Zuma bisa dogaro da tsarin mulkin kasar da ke haramta takara ga wanda ya yi zaman gidan wakafi na tsawon watanni 15 kan rashin da'a ga umarnin kotu.

https://p.dw.com/p/4g4hA
Jacob Zuma a wani zaman kotu a 2023 a Afrika ta Kudu
Jacob Zuma a wani zaman kotu a 2023 a Afrika ta KuduHoto: Kim Ludbrook/AFP/Getty Images

To sai dai Jam'iyyar uMkhonto we Sizwe (MK) ta Afrika ta Kudu ta nuna rashin jindadinta kan soke takarar tsohon shugaban kasar a zaben gama-gari na 'yan majalisar dokokin kasar da za a gudanar a wannan wata na Mayu. A kundin tsarin mulkin kasar duk wanda ya yi zaman gidan wakafi na watanni 15 bisa rashin da'a ga kotu, ba zai tsaya takara ba.

Karin bayani: Zaben Afrika ta Kudu: Zuma ya daukaka kara 

Dama dai hukumar zaben kasar ta soke takarar Jacob Zuma, wanda daga bisani wata kotu ta tabbatar masa da takarar shugabancin kasar. Daga bisani hukumar zaben kasar ta daukaka kara zuwa kotun kundin tsarin mulkin kasar.

Karin bayani: Tsohon shugaban Afirka ta Kudu ya tsallake rijiya da baya

Zuma wanda ya raba-gari da jam'iyyarsa ta ANC tun bayan da aka tsige shi daga mumakinsa gabanin zaben 2018, ya kafa wata sabuwar jam'iyya (MK), domin kalubalantar jam'iyyar ANC mai maulkin kasar wacce kuma ta yi gwagwarmayar kawo karshen mulkin wariyar launin fata a kasar. Sai dai farin jinin jam'iyyar na disashewa shekaru 30 bayan gwagwarmaya.