Kudirin aniyar rikakafin cutar Ebola
April 10, 2014Hukumar lafiya ta duniya WHO, tare da hadin gwiwar Red Cross, da ma Unicef, sun amince su kara daukan matakan rigakafin kamuwa da cutar zazzabin Ebola da ke ci gaba da wakana a kasashen yammacin Afirka, musamman ma, a kasar Guinea inda tutar tafi kamari.
Wadannan mayan kungiyoyin na duniya 3, sun yi wannan bayani ne cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar a wannan Alhamis din (10.04.2014), inda suka ce za'a fara bayar da horo, da kuma fadakarwa ta kafofin yada labarai kan matakan rigakafin kamuwa da cutar ta Ebola, wadda kawo yanzu ta yi sanadiyar rasuwar a kalla mutane 101 a kasar ta Guinea daga cikin mutane157 da suka kamu da wannan cuta, yayin da a kasar Liberiya mutane 10 suka rasu daga cikin 21 da suka kamu da cutar.
Sai dai wasu da ake zaton wannan cutace ta kama su a kasashen Mali da Saliyo, bincike ya nunar da cewa ba wannan cuta ba ce.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mohammad Nasiru Awal