Hari a masallaci a Saudiyya
August 6, 2015Talla
Wannan harin kunar bakin wake ya hallaka mutane 17 a birnin Abha da ke a Kudu maso Yammacin kasar Saudiyya kamar yadda rahoton gidan talabijin na al-Ekhbariya a kasar ta Saudiyya ya nunar.
Wani jami'i a ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Saudiyya ya fada wa kamfanin dillancin labaran Associated Press cewa bam din ya fashe ne a wani masallaci da jami'an tsaro ke gudanar da ibada.
Jami'in da baya so a bayyana sunansa, a zantawa da kamfanin dillancin labaran na AP ya ce wannan masallaci mallaki ne na ma'aikatar harkokin cikin gida da suka shafi ayyukan gaggawa da ke a birnin Abha. Sai dai jami'in bai bayyana ko masallacin a cikin ma'akatar harkokin cikin gida yake ba.