Kungiyar AU ta dakatar da Sudan
June 6, 2019Matakin na zuwa ne a lokacin da likitoci a Sudan ke cewa adadin wadan da suka mutu a artabu da jami'an tsaro yayin zanga-zanga ya haura 100, amma hukumomin kwamitin mulkin soji ta karyata adadin.
Shugabannin kungiyoyin farare hula sun yi fatali da bukatar kwamitin mulkin soji na sake shiga tattaunawa domin samun dai-daito, inda kungiyoyin ke neman a hukunta wadan da suka aikata kisa.
Firaministan Habasha Abiy Ahmed na da niyyar sulhunta bangarorin da ke rikici da juna a Sudan, yayin da kungiyar Amnesty Intternational ta bukaci kasashen duniya su kawo dokin gaggawa kan rikin kasar da ke kashe fararen hula.
Tuni ma kasashe kamar Birtaniya da Majalisar Dinkin Duniya suka fara janye jami'ansu daga kasar Sudan, bayan da zaman kwamitin sulhu ya gaza samar da mafita kan halin da kasar ke ciki.