Kungiyar Hamas ta cika shekaru 30
December 14, 2017Shugaban kungiyar Hamas na farko, Ahmad Yaseen ya tsara manufofin kungiyar kan akidar, Abin da aka kwacema da karfi, ba ka kwatoshi sai da karfi, lamarin da ya sanya kungiyar zama a kullum cikin shirin ko-ta-kwana,don tinkarar kasar Isra'ila a fagen daga. Duk da kisan gillar da Isra'ila tai ta yi wa shugabanninta, irin su Ahmad Yaseen da Salah Shahadah da Rantisi da sauransu, da kuma ayyana yaki har sau uku kan yankin Gaza da gwagwarmayar kungiyar ta Hamas a cikinsa ya tilasta wa Isra'ila ficewa ba girma ba arziki daga birnin. Tare kuma da killaceshi da Isra'ilan da Masar suka yi, duk da hakan, kungiyar ta Hamas, ba ta fito ba sai da ta shirya, ta ci gaba da jajaircewa kan akidarta ta kwatar illahirin yankunan Falalsdinawa daga mamayar Isra'ila da karfin tuwo.