Taliban na kara tura yara fagen yaki a Afghanistan
February 17, 2016Wani rahoto da kungiyar kare hakin dan Adam ta Human Rights Watch ta wallafa ya ce kungiyar Taliban a Afghanistan na kara tura yara fagen daga. Kungiyar ta ce a bara akalla yara 100 nekuma aka yi amfani da su a matsayin soji a lardin Jardara mai fama da rikici. Binciken da kungiyar ta kare hakin dan Adam ta yi, ya fi mayar da hankali ne a yankin Kundus, inda masu kaifin kishin addini ke amfani da makarantun Islamiyya a matsayin sansanonin horas da yara aikin soja, inda kuma ake nuna musu sarrafa makamai da harhada bam da kuma dana shi. Kungiyar ta ce musamman iyaye matalauta sun fi tura 'ya'yansu wadannan makarantu inda ake ba su abinci da tufafi kyauta. Tun suna 'yan shekaru shida ake fara daukarsu a makarantu, daukacin sojoji kananan yaran 'yan shekaru 13 ne zuwa 17.