Kungiyar IS ta ce ta kona dan Jordan da ta ke rike da shi
February 3, 2015Talla
Magoya bayan mayakan kungiyar IS mai fafutukar kafa daular musulunci, sun nuno wasu hotuna ta shafin Intanet dake nuna suna kona wani da ran sa wanda suka matukin jirgin saman nan ne dan kasar Jordan, Muath Al Kasaesbeh, wanda suke garkuwa da shi.
Koda yake ba a kaiga tabbatar da sahihancin fotunan na shafin Intanet din ba, mayakan na IS, sun nuno wani dake konewa ne a tsaye cikin wani bakin keji. Matukin jirgin na Jordan Muath Al Kasaesbeh dai, ya shiga hannun mayakan ne tun lokacin da jirgin da yake tukawa ya fadi a kusa da Raqqa na kasar Syria cikin watan Disamaban bara.
Kasar Jordan dai ta nuna aniyar amincewa mika wata 'yar Al Qaeda Sajida Al-Rishwa dake tsare a kasar, musayar da kungiyar ce ta bukace ta.