Kungiyar IS ta sanar da sabon shugaban Boko Haram
August 3, 2016Jaridar kungiyar nan da ke da'awar kafa daular Musulunci a Iraki da Siriya ta sanar da sabon shugaba ga reshenta da ke yankin yammacin Afirka da aka fi sani da kungiyar Boko Haram. Sai dai sabon jagoran na masu kaifin kishin addinin ya yi alkawarin cewa ba za su farma masallatai da kasuwannin da Musulmi ke amfani da su ba.
Jaridar al-Nabaa ta harshen Larabci a wannan Larabar ta ce Abu Musab al-Barnawi shi ne sabon shugaban Boko Haram. Rahoton bai fadi matsayin tsohon shugaban Boko Haram Abubakar Shekau a yanzu ba.
Jacob Zenn manazarcin al'amuran yau da kullum ya ce sanarwar na nuni da wani juyin mulki da kungiyar Ansaru da ta balle ta yi wa Boko Haram da kuma ke bin wani salon kungiyoyin tarzoman Islama masu barin akidar kungiyar Al-Kaida zuwa ta kungiyar IS.
Kungiyar Ansaru dai ta yi suna wajen garkuwa da baki. Ta raba gari da Boko Haram saboda ta ki amincewa da kisan fararen hula musamman Musulmi ba gaira ba dalilai.