1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar NATO na duba makomar Mosul

October 25, 2016

Duk da ma irin sabanin da ke tsakanin Turkiya da Iraki Turkiya ta bayyana cewar za ta ba da tata gudummawa a wannan yaki kamar yadda Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya bayyana.

https://p.dw.com/p/2RgRh
Paris - Verteidigungsminister der Anti-IS-Koalition beraten in Paris
Mambobin kasashen da ke kawancen yakar IS a taron ParisHoto: REUTERS/C. Platiau

Ministocin kula da harkokin tsaro na  NATO sun yi taro a ranar Talatan nan a birnin Paris na Faransa domin tattauna makomar birnin Mosul na Iraki a kokarin da ake yi na kubutar da birnin daga hannun kungiyar masu yin jihadi ta IS, tare da kuma  da duba ci gaban kai hare haren.Taron dai na zuwa ne mako daya bayan kaddamar da hare-hare na taron dangi a kan 'yan tawayen na IS a Gabashin Iraki.

An yanke shawara yin wannan taro ne kan makomar  birnin na Mosu na Iraki da ma wasu sauran sassan kasar da har yanzu ke hannun 'yan tawayen tun a makon jiya. Kuma wannan na nuna mahimmanci da kasashen Yammacin duniya suke da shi a kan Iraki game da wasu muradunsu duk kuwa da irin banbance-babancen da ke a tsakanin kasashen Yammacin duniyar a kan yakin na Iraki.

AWACS und NATO Symbole
Dakarun da ke kawancen yakar IS Hoto: AP

Duk da ma irin sabanin da ke tsakanin Turkiya da Iraki Turkiya ta bayyana cewar za ta bada tata gudummawa a wannan yaki kamar yadda Shugaba Recep Tayyib Erdogan ya bayyana wanda ya ce sojojin kasar za su shirya kai sumame ta kasa a Arewacin Irakin. Abin da bisa ga dukkan alamu Firaministan Iraki Haidar Al Abadi ke kallo a matsayin wata barazana ga Kurdawan kasar.

Ministocin harkokin tsaron na kasashen Amirka da Kanada da Faransa  da Birtaniya da Jamus da Beljiyam da Italiya da Holland da Danmak za su samu karin bayyani da shugabannin yanki na kasashen a game da dubarun da za a kara yin amfani da su domin yakar kungiyar ta IS don sake kwato wasu yankunan da har yanzu suke cikin hannun kungiyar.

Bayan dai gaggarumar nasarar da aka samu a Irakin a shekara ta 2014 a yanzu kasar ta rasa kusan rabin yankunan da ke a gabashi kasar wadanda ke cikin hannu 'yan tawye na  IS.