1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar NATO za ta girke dakaru dan tinkaran kasar Rasha

Abdul-raheem HassanJuly 8, 2016

Kungiyar kawancen tsaron ta kuduri aniyar kare iyakokinta na gabashin Turai daga duk wata barazana daga Rasha.

https://p.dw.com/p/1JM4g
NATO Gipfel in Warschau Stoltenberg , Obama und Duda
Daga hagu zuwa dama: Stoltenberg babban sakataren NATO da Obama na Amirka da kuma shugaban Poland DudaHoto: Reuters/Agencja Gazeta/S. Kaminski

A wannan Jumma'a shugabannin kasashen kungiyar kawance ta NATO suka gana a birnin Warsaw na kasar Poland da nufin tattauna batutuwan da suka shafi harkar inganta tsaro da ma dabbaka tsarin dimokradiyya a tsakanin kasashen. Kawancen dai zai kaddamar da girke dakaru dubu uku zuwa dubu hudu a kasashen Estoniya, da Lithuaniya, da Latviya da kuma gabashin Poland wanda zai kasasnce a tarihin kungiyar tsaron da za ta jibge sojojinta a matsayin hannunka mai sanda ga kasar Rasha.

Da yake jawabi a taron, Shugaban Amirka Barack Obama, ya bayyana matsayin kasarsa a wannan tafiya.

"Ina sanar da ku cewa Amirka na kan gaba wajen daukar matakan da suka dace da zai karfafa kawancen kungiyar tsaro ta NATO. Muna sa rai cewa burinmu zai kai gaci don kawar da rashin tsaro a tsakiyar Turai da gabshinta ke fama da shi."