NATO za ta kara kaimi a Afghanistan
July 9, 2016Talla
Shugabannin kasashe guda 28 na kungiyar tsaro ta NATO da ke yin taro a birnin Warsaw na kasar Poland a kwanaki na biyu jere sun tattara kudade kusan biliyan daya na dala, domin taimaka wa Amirka a cikin shekaru uku masu zuwa a game da shirinta na tsara rundunar sojojin Afghanistan. Jens Stoltenberg shi ne babban sakataren kungiyar tsaron ta NATO da ya yi karin haske.
Ya ce: ''Da farko mun amince mu cigaba da kawo wa rundanar kawance ta dakarun da ke a Afghanistan dauki har bayan wannan shekara da muke ciki har zuwa shekara ta 2020.''
A badi dai ana sa ran dakarun kasashen kawance hade da Amirka a Afghanistan din za su kai har dubu goma sha biyu.