Shekaru 60 da kafa kungiyar OPEC
September 14, 2020An dai kafa kungiyar OPEC din ta kasashe masu arzikin man fetur a duniya ne da nufin taka birki dangane da rawar da kamfanonin Amirka ke takawa a cikin masana'antar man mai tasiri. Sai dai kuma bayan shekaru 60 tana taka rawa a kokari na daidaiton lamura a cikin masana'antar, ra'ayi na bambanta a cikin Tarayyar Najeriya, dangane da rawa da ma tasiri na kungiyar a cikin masana'antar mai ta kasar.
Karin Bayani: Najeriya: Martani kan farashin man fetur
OPEC din dai ta taka rawar daidaita farashi da ma yawan man da kasashe na kungiyar ke iya samu da nufin tsari da tabbatar da cin moriyar hajar man tsakanin kasashen kungiyar. Kaso 90 cikin dari na arzikin Najeriyar dai na zuwa ne daga hajar man da kasar ta share shekara da shekaru tana samarwa. Kuma OPEC na zaman ta kan gaba wajen tabbatar da kyautata farashin man da ya taka rawa wajen ginin kasar tun bayan 'yancin kai ya zuwa ga annobar COVID-19
Lawal Habib dai na zaman masanin tattalin arzikin da ya ce OPEC ta zamo uwar da ta dauki lokaci tana shayar da kasar a kan hanyar dora ta zuwa girman da take da bukata. Kokari na samar da kariya ga batu na fasahar mai ko kuma mai da ta zuwa 'yar mowa dai, kariyar ta OPEC ce ake yi wa kallon ummul aba'isin mantawar kasar da mayar da hankali ya zuwa sassa dabam-dabam na tattalin arzikin da take da bukata baya.
Kafin rikicin na faduwar farashin man fetur gami da lalacewar ababen more rayuwa dai, man na zaman jagora na walwala da kuma nuna halin ko in kular a cikin harkokin noma da ma'adinai da ma bukatar gina masana'antu na sarrafa a tsakanin al'umma. Kuma a fadar Dakta Garba Ibrahim Malumfashi da ke zaman tsohon mashawarci a kungiyar ta OPEC, hakan ya janyowa kasar koma baya na lokaci mai tsawo, idan aka kwatanta da kawayen samun 'yancinta na baya.
Karin Bayani: Gwamnatin Najeriya ta cire tallafin mai
Rawar hajar man wajen baro Najeriyar a cikin fatara dai, daga dukkan alamu na da ruwa da tsaki da sauyi na rawa da kila ma sababbin manufofin 'yan mulki na kasar.