Kungiyar taimakawa Zawarawa a Maradi
November 2, 2016Malam Rabi'u shi ne shugaban wannan kungiya ya kuma
bayana mini dalilansu na kafa wanan kungiya ta taimakon zawaru()
Ayukan kungiyar dai sun hada da tallafama Zawarawa a fannoni da dama
kamar yadda Hajiya Makka Shawai, daya daga cikin shugabannin kungiyar ta
bayyana.
Mata Zawaru da dama ne suka samun tallafi ta hanyar shiga wanan
kungiya kuma sun bayyana farin ciki da jin dadinsu kan ci gaban da suka samu.
Yanzu haka wasu maza masu neman aure sun fara kai ziyarta a cibiyar
kungiyar don gani da ido ayyukan alherin da wanan kungiya ta ke
shinfidawa. Alhaji Ismael wani dan kasuwa ne da ya leka, kuma acewarsa abin ya
birgeshi kuma har ya gano matar aure.
Hausawa na cewa ko kana da kyau ka kara da wanka. Kungiyar dai na
bukatar tallafi da goyon bayan masu hannu da shuni da ma al'umma don
fadada ayyukanta a fadin kasa .