1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Taliban ta kai mummunan hari a Kabul

Gazali Abdou TasawaAugust 1, 2016

A Afghanistan kungiyar Taliban ta dauki alhakin harin da aka kai da wata babbar mota da aka dana wa bam a Hotel Northgate da ke birnin Kabul inda baki fararan hula da sojoji 'yan asalin kasashen waje ke yawan sauka.

https://p.dw.com/p/1JZSu
Afghanistan Angriff auf Wohnanlage für Ausländer in Kabul
Hoto: Reuters/O. Sobhani

Rahotanni daga babban birnin na kasar Afghanistan wato Kabul na cewa an ji karan tashin bam din a kusan duk fadin birnin da karan harbe-harben bindigogi a wurin da aka kai harin inda daga bisani tarin jami'an tsaro suka ja daga.

Bayan share awoyi ana fafatawa, hukumar 'yan sandar birnin na Kabul ta sanar da mutuwar maharan su uku. Amma kuma ta ce an samu mutuwar jami'in dan sanda daya a yayin da wasu hudu suka ji rauni.

Sai dai kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya sanar da cewa sojojin Amirka sama da 100 suka halaka wasu kuma sun ji rauni a cikin harin.